Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wolves ta dauki aron Francisco Trincao daga Barcelona
Wolves ta dauki aron dan kwallon Portugal, Francisco Trincao daga Barcelona da yarjejeniyar sayar mata da shi, idan ya taka rawar gani.
Cikin yarjejeniyar da suka kulla, Wolves za ta iya sayen dan kwallon mai shekara 21 nan gaba, amma ba matsi sai idan ta gamsu da rawar da zai taka mata.
Dan kwallon ya koma Sifaniya da taka leda daga Braga ta Belgium a kakar 2020.
Trincao ya buga wa Barcelona gasar Lik 28 a kakar da aka karkare, ya kuma ci kwallo uku ya bayar da biyu aka zura a raga, ya buga Champins League wasa bakwai.
Shine na biyu da ya koma Wolverhampton don tunkarar kakar 2021-22, bayan da ta dauki dan wasan tawagar Colombia, mai tsaron baya, Yerson Mosquera.