Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dani Carvajal: Dan kwallon Sifaniya ya buga wa Real Madrid wasa na 200 a La Liga
Real Madrid ta buga wasa 3-3 a gidan Levante a karawar mako na biyu a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.
Gareth Bale ne ya fara ci wa Real kwallo minti biyar da fara tamaula, bayan da suka koma daga hutu ne Alaves ta farke ta kuma kara ta hannun Roger Marti da kuma Jose Campana.
Daga baya Real ta farke ta hannun Vinicius Junior, sai dai minti shida tsakani Alaves ta kara na uku ta hannun Rober, sannan aka bai wa dan kwallonta Aitor jan kati, saura minti biyu a tashi karawar.
Tun kan a kori dan wasan Alaves, Real Madrid ta farke na ukun ta hannun Vinicius Junior kuma na biyu da ya ci a karawar, sanna na uku a La Ligar bana.
Wannan shine karon farko da Gareth Bale ya ci wa Real Madrid kwallo tun bayan kwana 578, kwallon karshe da ya ci wa kungiyar shine a Copa del Rey da Unionistas ranar 22 ga watan Janairun 2020.
Wannan shine wasa na 200 da Dani Carval ya yi wa Real Madrid wadda ya fara daga matasan kungiyar, ya kuma fara yi mata tamaula cikin shekarar 2013.
A kakar bara Real Madrid ta ci Levante har gida a wasan farko a bara da 2-0 ranar 4 ga watan Oktoban 2020.
Sai dai kuma a wasa na biyu da suka fafata a La Liga a bara ranar 30 ga watan Janairun 2021, Real ta yi rashin nasara a gida da ci 2-1.
Real Madrid za ta buga wasa na uku a jere da za ta ziyarci Real Betis ranar 28 ga watan Agusta.