Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi: Watakila kyaftin din Argentina ya fara buga wa PSG wasa ranar Lahadi
Watakila Paris Saint Germain ta saka Lionel Messi ya buga mata wasa a karon farko, tun bayan da ya koma kungiyar a bana.
Ranar Lahadi PSG za ta ziyarci Reims a wasan mako na hudu a gasar Faransa ta Ligue 1 ta bana.
PSG ta ci dukkan wasa ukun da ta buga a bana a Ligue 1, ita ce kan gaba a teburi, duk da Neymar da Messi ba su buga mata gumurzun ba.
Watakila lokaci ya yi da ya kamata koci Mauricio Pochettino ya fara saka kyaftin din Argentina, wanda rabon da ya buga tamaula tun bayan Copa del Rey da suka lashe a Brazil a bana.
Messi wanda ya koma Faransa da taka leda a bana, bayan da Barcelona ta fada cikin matsin tattalin arziki, yana atisaye a PSG, wadda ta gabatar da shi gaban magoya bayanta.
Cikin sabbin 'yan wasan da PSG ta dauka a bana, Gianluigi Donnarumma ya yi zaman benci a ranar Juma'a a wasan da ta doke Brest 4-2.
Yayin da Achraf Hakimi da kuma Georginio Wijnaldum sun buga wa PSG dukkan fafatawa ukun da ta yi a Ligue 1 na bana.
Kawo yanzu Messi da mai tsaron ragar tawagar Italiya, Donnarumma ne ba su buga wa PSG kwallo ba, cikin sabbin 'yan kwallon da ta dauka a bana.
Wani dan kwallon da shima bai fara yi wa PSG tamaula ba, shine Sergio Ramos, wanda ke jinya da ba a fayyace lokacin da zai murmure ba.
Messi ya koma Paris St Germain, bayan shekara 21 da ya yi a Camp Nou, bayan da Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki.
Tun makon da ya wuce shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sanar cewar bashi ya yi wa kungiyar katutu da ya kai fam biliyan 1.35.
Matsin tattalin arzikin da Barcelona ta fada ne ya sa ta kasa tsawaita kwantiragin Messi, wanda ya amince da rage rabin albashin sa.
Tuni kyaftin din tawagar Argentina ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a PSG da sharadin za a iya tsawaitata kaka daya nan gaba.