Kasuwar cinikin ƴan ƙwallo: Makomar Mbappe, Ronaldo, Kounde, Dalot, Trippier, Edouard, da Martinez

An wallafa

Cristiano Ronaldo zai zama ɗan wasa mafi yawan albashi a tarihin gasar Premier League da zarar ya kammala komawarsa Manchester United daga Juventus. (Telegraph - subscription required)

Real Madrid ta bai wa PSG yau Lahadi ta yanke hukunci kan tayin da ta yi wa Kylian Mbappe. Madrid ta ce ba za wuce tayin fam miliyan 163 da ta yi ba kan ɗan wasan mai shekara 22. (Le Parisien - in French)

Fatan Chelsea na sayen mai tsaron bayan Sevilla Jules Kounde ya samu giɓi, bayan da ƙungiyarsa ta ƙara masa kuɗi zuwa fam miliyan 68.5. (Telegraph - subscription required)

A Jamus kuwa, Borussia Dortmund na fatan sayen mai tsaron bayan Manchester United Diogo Dalot. (Sky Sports)

To amma wata majiya ta ce Dalot na son ci gaba da zama a United don gwada sa'arsa. (Goal)

Manchester United na shirin neman mai tsaron bayan Ingila da ke wasa a Atletico Madrid Kieran Trippier da ƙungiyarsa ke neman fam miliyan 34 kansa. (AS via HITC)

Tottenham ta fara neman mai tsaron bayan Barcelona Emerson Royal mai shekara 22, da nufin sayar da Sergie Aurier. (Telegraph - subscription required)

Juventus na dab da sake dauko ɗan gaban Everton Moise Kean aro tsawon shekara biyu da nufin sayen shi din-din-din. (Sky Sports)

Ita kuwa Everton ta nuna sha'awar sayen mai tsaron bayan Arsenal Ainsley Maitland-Niles mai shekaru 23 a matsayin aro. (Sky Sports)

Anan kuma Reading na kan tattaunawa da Chelsea don sayen ɗan wasan tsakiyarta Danny Drinkwater. (Reading Chronicle)

Ɗan wasan tsakiyar Faransa Tiemoue Bakayoko mai shekaru 27 ya isa Italiya don duba lafiyarsa, bayan aminta da yarjejeniyar shekara biyu a matsayin aro daga Chelsea zuwa Milan. (Football Italia)

Idan muka leƙa maƙwabtan Milan din wato Inter, rahotanni na cewa dan wasan gabanta Lautaro Martinez mai shekaru 24 ya aminta da tsawaita zamansa a ƙungiyar. (Gianluca Di Marzio - in Italian)