Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester City: Ederson ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya
Mai tsaron ragar Manchester City, Ederson ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya da za ta kare a kungiyar a 2026.
Ederson, wanda ya koma City a 2017 ya lashe kofi uku na Premier League a kungiyar da ya yi wa wasa 194.
Dan kwallon tawagar Brazil, shine na biyar da ya tsawaita kwantiraginsa a Etihad a bana, bayan Kevin de Bruyne da Fernandinho da John Stones da kuma Ruben Dias.
Tun lokacin da ya koma Etihad da taka leda, Ederson ya lashe FA Cup da Carabao Cup hudu da kuma Premier League uku.
Cikin fafatawa 194 da ya yi wa City, Ederson bai bari kwallo ya shiga ragar sa ba a wasa 95, kuma sau biyu yana lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga a Premier League.