Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Japan ta fasa karbar bakuncin Fifa Club World Cup a bana
Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta ce Japan ta janye daga karbar bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta bana, saboda tsoron yada cutar korona.
Ana buga wasannin tsakanin zakarun nahiyoyi duniya shida a kowacce shekara cikin watan Disamba.
''FIFA tana tabbatar da cewar hukumar kwallon kafar Japan ta sanar mata da cewar da janye wa daga karbar bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta 2021, sakamakon cutar korana da ke kara ruruwa a kasar.'' in ji sanarwa.
Japan ce ta karbi bakuncin wasannin da aka yi a 2016, kuma ta yi niyyar gudanar da fafatawar bana don murnar bikin cika shekara 100, in ji wasu rahotanni.
Gwamnatin Japan ta kara sa dokar ta baci a wasu yankunan kasar tun daga ranar Alhamis, bayan da annobar ke kara baraza a kasar.
Bayern Munich ce ke rike da kofin bara da ta lashe kuma na biyu a tarihi, bayan da ta doke Los Tigres ta Mexico da ci 1-0.
Real Madrid ce ta daya mai hudu a jerin masu yawan lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi.