Real ta koma Santiago Bernabeu karon farko bayan kwana 560

An wallafa

Filin wasa na Santiago Bernabeu zai karbi wasan La Liga a bana a karon farko tun bayan kwana 560 ranar Lahadi.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta Vigo a wasan mako na hudu a gasar La Liga, wasan farko da za ta yi a filin a bana.

Rabonda a taka leda a filin tun ranar 1 ga watan Maris din 2020 a lokacin da Real Madrid ta doke Barcelona a karawar El Clasiso kwana 560 kenan.

Real Madrid ta ci gaba da wasannin gida a filinta da ke Valdebebas shekara daya da rabi, inda ta dauki a La Liga a lokacin da aka dunga buga wasannin don gudun yada cutar korona.

Ma'aikata 800 ne ke aiki a kowacce rana don ganin an fadada filin wasa na Bernabeu da zai ci 'yan kwallo dubu 80, haka aka ci gaba da aiki har cikin lokacin da ake dokar kulle kai domin ganin filin an kammala shi kamar yadda aka tsara.

Cikin aikin na kwana 560 don fadada Bernabeu, Real ta karbo bashin Yuro miliyan 575 domin cimma burinta.

Real Madrid wadda ta dade bata dauki fitatcen dan kwallo ba don tsuke bakin aljihu ta dauki La Liga a tsawaon lokacin, yayin da sauran kofuna suka yi mata wahalar dauka har da kakar da ta wuce.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aiki, bayan kammala kakar da ta wuce, inda ta maye gurbin sa da Carlo Ancelotti.

Real ba ta tsawaita kwantiragin Sergio Ramos ba, wanda ya koma Paris St German da taka leda a karshen kakar da ta karkare.

Haka shima dan kwallon tawagar Faransa Raphael Varene abokin taka leda da Ramos a tsaron baya, ya koma taka leda a Manchester United a bana.

Sai dai Real wadda kasuwancin da take ke tafiya ba matsala ta dauki David Alaba, wanda yarjejeniyar sa ta kare a karshen kakar da ta wuce, sannan ta sayo Edourdo Camavinga da Rennes a bana, bayan da Paris St Germain ba ta sallama mata Kylian Mbappe ba.

Kungiyar Barcelona ta fada matsin tattalin arziki da ta kai ta kasa tsawaita kwantiragin Lionel Messi, wanda ke taka leda a PSG a kakar nan.