Mohamed Salah ya ci kwallo na 100 a Premier League

Mohamed Salah
Bayanan hoto, Mohamed Salay ya ci wa Chelsea kwallo biyu, sannan ya ci gaba da zura kwallaye a Liverpool
An wallafa

Mohamed Salah ya zura kwallo na 100 a raga a gasar Premier League a karawa da Leeds United ranar Lahadi.

Liverpool ta ziyarci Leeds United domin buga wasan mako na hudu a gasar Premier League, inda Salah ya fara cin kwallo a minti na 20 da fara tamaula.

Kwallon da Salah ya ci shine na 100 da ya zura a raga a Premier League, kuma na biyar da ya yi wannan bajintar a karancin wasanni, bayan Alan Shearer a wasa na 124, sai Harry Kane a karawa ta 141 da kuma Sergio Aguero a fafatawa ta 147.

Na hudu a wannan namijin kokarin shine Thierry Henry da ya ci kwallo na 100 a Premier League a wasa 160, sannan Salah wanda ya ci a karawa ta 162.

Salah ya koma Chelsea da taka leda a 2014, wadda ya fara buga wa wasa ranar 8 ga watan Fabrairu da ya shiga sauyin dan kwallo a fafatawa da Newcastle United.

Wasa bakwai tsakani Salah ya fara ci wa Chelsea kwallo ranar 22 ga watan Maris a karawar da ta yi da Arsenal a Stamford Bridge wanda ya canji dan wasa, inda Blues ta ci 6-0.

Ranar 5 ga watan Afirilu Salah ya fara cin kwallo a wasan da Chelsea ta ci Stoke City 3-0, ya kuma samu fenariti, sannan ya bar da kwallo da aka ci na uku a fafatawar.

Bayan kwallo biyu da Chelsea ya ci wa Chelsea ta bayar da aron sa ga Fioentina a 2015 daga nan ta bai wa Roma aron Salah daga baya ta sayar mata da shi a 2016, daga baya Liverpool ta dauko shi a kakar 2017.

Dan wasan tawagar Masar ya fara cin kwallo a wasan Premier a karawar farko da ya fara yi wa Liverpool da ta tashi 3-3 da Watford ranar 12 ga watan Agusta.

Ranar 24 ga watan Agusta Salay ya ci wa Liverpool kwallo a Champions League a karawa da Hoffenheim na farko da ya ci a Anfield.

Kwana uku tsakani Salah ya ci kwallo ya kuma bayar an zura a raga a wasan da Liverpool ta doke Arsenal.

Mohamed Salah ya lashe kyautar takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League a kakar 2017-18 da kuma 2018-19.