Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Phillips da Olmo da Fofana da Rodriguez da kuma Dembele

Kalvin Phillips
Bayanan hoto, Kalvin Phillips dan kwallon Leeds United mai buga mata wasannin tsakiya
An wallafa

Kocin Manchester City Pep Guardiola na son kungiyarsa ta dauko masa dan kwallon Leeds United Kalvin Phillips, mai shekara 25 a farkon kakar badi. (Fichajes, in Spanish)

Barcelona na shirin yin zawarcin dan kwallon RB Leipzig Dani Olmo - yayin da Manchester United da Juventus da kuma Bayern Munich ke son su ma su sayi dan kwallon mai shekara 23. (Marca, in Spanish)

Dan kwallon Leicester City mai tsaron baya, Wesley Fofana, mai shekara 20, ya ce Real Madrid ita ce babbar kungiyar tamaula a duniya, kuma yana fatan wata rana ya buga wasa a kungiyar. (YouTube, via Marca)

Everton ta kasa sayar da dan wasan tawagar Colombia, James Rodriguez mai shekara 30 saboda fam 25,000 da yake dauka a duk mako. (Football Insider)

Kungiyoyin Premier League na son daukar dan wasa Alexander Isak, mai shekara 21, duk da dan kwallon tawagar Sweden ya sanya hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Real Sociedad. Arsenal da Chelsea na son daukarsa. (Fichajes via Teamtalk)

Tottenham Hotspur ta bude kafar tattaunawa da Ajax kan daukar mai shekara 20, mai tsaron bayan tawagar Netherlands, Jurrien Timber. (Todofichajes in Spanish)

Barcelona na shirin tsayar da ranar tattaunawa da wakilin Ousmane Dembele kan tsawaita yarjejeniyar dan wasan mai shekara 24 a Camp Nou, (Mundo Deportivo, in Spanish)

Barcelona na sha'awar salon taka ledar dan kwallon AC Milan Kessie, mai shekara 24 - Za kuma ta fuskanci kalubale daga wajen Liverpoolda Tottenham da kuma Paris St-Germain wadanda suma suna son daukar dan kwallon Ivory Coast. (Mundo Deportivo, in Spanish)

Dan wasan tawagar Serbia, mai shekara 21, Dusan Vlahovic, wanda Tottenham da kuma Atletico Madrid suka yi zawarci a bana, na tattaunawa kan batun tsawaita yarjejeniyar zamansa a Fiorentina. (Fabrizio Romano)

Dan kwallon Faransa, Houssem Aouar, mai shekara 23, ya yi watsi da batun da ake cewar zai koma Arsenal wanda ya ce yana son taimakawa Lyon ta samu gurbin shiga Champions League. (Metro)