Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alex Iwobi: Na kara samun kwarewa a karkashin Benitez
- Marubuci, Daga Oluwashina Okeleji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai labaran wasanni daga Nigeria
- An wallafa
Dan wasan tsakiya na Najeriya da Everton Alex Iwobi ya ce ba shi da haufi ya kara samun kwarewa a karkashin mai horar da kungiyar Rafael Benitez da ya kama aiki a watan Yuli.
Iwobi mai shekara 25 ya je Everton daga Arsenal a 2019, inda ya kasa samun gurbi na din-din-din a 'yan wasa 11 na farko.
A karkashin Benitez dan kasar Sifaniya, Iwobi ya ci wa Everton kwallo daya a wasanni bakwai, ya kuma taimaka aka ci daya a kakar bana.
A hira da Sashen Wasanni na BBC Africa Iwobi ya ce "Ina ji a jikina cewa na kara samun kwarewa a karkashin samun sabon kocinmu, saboda yana da kwarewa sosai don ya yi aiki da 'yan wasa da kungiyoyin daban-daban.
"Da ya zo ya fada mini bangaren da nake da nakasu kuma yanzu haka ina ganin ci gaba."
"Idan aka ce kana karkashin koyarwar kwararren mai horarwa da ya yi aiki da manyan 'yan wasa za ka yi amfani da damar ne ka kara kwarewa."
A Arsenal Iwobi ya ci kwallaye 15 a wasanni 149, amma komawarsa Everton a karkashin Marco Silva da Carlo Ancelotti dan wasan bai haska ba sosai.
Sai dai Iwobi wanda ya buga wa tawagar matasan Ingila ya yarda cewa yana bukatar kara hobbasa a wasu bangarori na wasansa a bana, lura da yadda Everton ta kara habaka fiye da yadda aka santa a baya.
"Na fahimci cewa muna wani mataki tare da wani sabon mai horarwa. Saboda haka dole ne mutum ya fada wa kansa gaskiya ya fahimci inda yake da nakasu ya gyara.
"Na san muhimmancin samun damar buga wasanni akai-akai a kungiya, saboda haka zabin da ya rage mini shi ne in zage damtse in canza salon wasana idan har zan iya yakin neman samun gurbin na din-din-din," in ji Iwobi.
Alex Iwobi ya buga wasanni 160 a gasar Premier, ya kuma buga wasanni 26 a Gasar Zakarun Turai, to amma fa ya kai shekarun da ya kamata a ce kwarewarsa ta fito sosai.
"Gaskiya ne na yarda cewa a shekara 25 ba ni da uzuri, to amma sa'ar da na yi ita ce ina wasa a karkashin mutumin da ya shirya fito da kwarewar 'yan wasansa a fili."
"A zahiri yake cewa Benitez ya sauya salon wasan Everton. Kuma a kashin kaina zan yi amfani da wannan damar in rika gwada wasu abubuwan akai-akai."
Iwobi ya taba wakilitar Ingila a matakin tawagar 'yan kwallo masu tasowa, kafin ya yanke shawarar buga wa Najeriya wadda ta taba lashe kofin nahiyar Afrika har sau uku.
Kuma kawo yanzu ya ci wa tawagar Super Eagles din kwallaye tara a wasanni 48.