Arsenal ta ragargaji Tottenham a wasan hamayya

Arsenal
An wallafa

Kungiyar Arsenal ta yi nasarar doke Tottenham da ci 3-1 a wasan Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Emile Smith-Rowe minti 12 da fara wasan, kuma matashin dan wasa da ya ci kwallo a wasan hamayya na birnin Landan mai shekara 21 da kwana 60 ranar Lahadi, tun bajintar da Alex Oxlade-Chamberlain ya yi a Satumbar 2014 mai shekara 21 da kwana 43.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci na biyu, sannan Bukayo Saka ya kara na uku a minti 34 da tsaka da karawar.

Shima Bukayo Saka ya zama matashin da ya ci kwallo, sannan ya bayar aka zura a raga a wasan na hamayya na birnin Landan mai shekara 20 da kwana 21 a ranar Lahadi, tun bayan kwazon da Cesc Fabregas ya yi a Satumbar 2007.

Sauran minti 11 a tashi daga karawar Tottenham ta zare kwallo ta hannun Heung-min Son.

Son Heung-Min ya yi sanadiyar zura kwallo biyar a wasa hudu a Premier League da Arsenal, wanda ya ci uku kawo yanzu ya kuma bayar da biyu aka zura a raga.

Kawo yanzu an zura kwallo uku a wasa uku a jere a ragar Tottenham a gasar Premier League ta bana a karon farko tun bayan Satumbar 2003.

Ranar 11 ga watan Satumbar 2021, Crystal Palace ta doke Tottenham da ci 3-0 a Selhust Park, Sai kuma Chelsea ta je gidan Tottenham ta ci 8-0 ranar 19 ga watan Satumba da wanda Gunners ta ci 3-1 ranar 26 ga watan na Satumba.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta 10 a teburin Premier League, bayan buga wasa shida, ita kuwa Tottenham ta yi kasa zuwa ta 11 a kasan teburi ita mai maki 11.

Karon farko da Arsenal ta hau kan Tottenham a teburin Premier League tun bayan 25 ga watan Oktoban 2020.

Ranar Alhamis 30 ga watan Satumba, Tottenham za ta karbi bakuncin NS Mura a gasar Europa Conference League, ita kuwa Arsenal wadda ba ta buga wasannin zakarun Turai a bana za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wani wasan hamayya ranar 18 ga watan Oktoba.