Harry Maguire: Babu takaddama tsakanina da Cristiano Ronaldo a Man Utd

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Harry Maguire ya fito fili ya bayyana cewa babu 'takaddama' tsakaninsa da Cristiano Ronaldo game da wanda ya fi dacewa a matsayin kyaftin din Manchester United.

Jaridar The Mirror ce ta bayyana cewa Maguire bai jin dadin yadda Ronaldo ke tasiri a tsakanin 'yan wasan United.

Maguire ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa babu rashin jituwa tsakanin 'yan wasa a Old Trafford.

"Na ga labaran karya da dama game da wannan kulob din, kuma wannan na cikinsu," Maguire ya rubuta.

Matakin Maguire na zuwa ne kwana guda bayan da Marcus Rashford ya caccaki masu cewa yana daga cikin 'yan wasan da ke zaman doya da manja da Ronaldo.

Shi ma dan wasan tsakiya Fred ya musanta batun rashin zaman lafiya tsakanin 'yan wasan United.