FIFA da UEFA sun dakatar da Rasha da kungiyoyinta

fifa uefa
An wallafa

Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya da kuma ta nahiyar Turai wato Uefa sun dakatar da tawagar kwallon kafar Rasha da kungiyoyin kwallon kafar kasar daga shiga kowace irin gasa.

Matakin na zuwa ne bayan hukumar shirya wasannin Olympics ta IOC, ta bukaci a kori Rasha da Belarus daga shiga wasannin tsalle-tsalle a fadin duniya.

Matakin na nufin Rasha ba za ta samu damar buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ba, da aka shirya za ta buga da Poland.

Hakama tawagar matan kasar ba za ta samu zuwa gasar cin kofin kasashen Turai ba.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Spartak Moscow an kore ta daga gasar Zakarun Turai ta Europa.

Bugu da kari Uefa ta sanar da soke yarjejeniyarta da kamfanin makamashin Rasha na Gazprom.

Sanarwar ta hada ka da Fifa da Uefa suka fitar ta ce ''duka Shugabannin biyu na fatan a samu maslaha a Ukraine, don kwallon kafa ta cigaba da zama wani ginshiki na samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al'umma.''

Fifa da Uefa sun dauki matakin ne bayan da Rasha tare da hadin kan Belarus ta kutsa Ukraine ranar Alhamis, abinda ya haifar da yaki da yanzu haka ake gwabzawa.

Tun da farko Fifa ta fada wa Rasha cewa za ta buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya ne da sunan 'Football Union of Russia', saboda kutsawa Ukraine da ta yi.

Hakama FIFA ta ce ba za ta yi amfani da tutar Rasha ba, kuma zata buga wasannin ne a wata kasa daban.

To amma tuni kasashe da dama sun bayyana cewa ba za su buga wasa da Rasha ba da ko ma wane irin suna ne, kuma a cewar su hukuncin da masu ruwa da tsakin suka yi mata bai yi tsauri ba.