Kamaru ta nada Song kocin Indomitable Lions

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Kamaru ta nada tsohon mai tsaron bayan kasar Rigobert Song a matsayin sabon kocin tawagar Indomitable Lions.
Ministan wasannin kasar ya fitar da sanarwar da ke cewa Song zai maye gurbin Antonio Conceicao, da ya kai tawagar zagayan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON da Kamarun ta karbi bakunci.
Rigobert Song ne dan wasan da ya fi buga wa Kamaru kwallo a tarihi da wasa 137, kafin ya yi ritaya a 2010.
Kazalika mai tsaron bayar ya tafi gasar cin kofin duniya sau hudu, ya kuma lashe kofin nahiyar Afrika sau biyu.
Song ya taba horar da Indomitable Lions a 2016, kuma shine ya tafi da kasarsa gasar Olympics a 2018.

Asalin hoton, Getty Images
Babban kalubalen da ke gaban sabon kocin a yanzu shine kai Kamaru gasar cin kofin duniya, idan har ya fitar da Aljeriya a wasan neman gurbin zuwa Qatar 2022 din da za a yi a watan Nuwamba.
Dama abokin wasansa Samuel Eto'o ne Shugaban Hukumar Kwallon kafar Kamaru, wanda hakan ke nufin Kamaru ta daura alhakin ci gaban kwallon kafarta a wuyan tsofaffin yan wasanta.























