Rikicin Ukraine: Hukumar tseren Formula One ta katse hulda da Rasha

An wallafa

Hukumar tseren motocin Formula One ta soke hulda da Rasha saboda ta kutsa Ukraine.

Hakan na nufin daga yanzu ta cire Rasha daga cikin kasashen da za rika karbar bakuncin gasar Grand Prix.

Sanarwar ta ce ''Formula 1 na tabbatar da cewa ta soke yarjejeniyar ta da Rasha, wadda a baya tana cikin jerin kasashen da za su rika karbar bakuncin gasar tseren Grand Prix.''

Rasha ce ta karbi bakuncin gasar a Sochi a 2014, kuma an shirya sake gudanar da gasar a Saint Petersburg a 2023.

Dama Formula One ta soke gudanar da gasar Grand Prix ta bana saboda rashin jituwa da aka samu a tsakanin manyan direbobin gasar.

Mai rike da kambun Max Verstappen da kuma Sebastian Vettel wanda ya taba cin gasar har sau hudu sun ce ba za su yi tsere a Rasha ba.

''A ra'ayi na ba zan tafi ba, Ina ganin ba dai-dai bane in yi tsere a Rasha.'' In ji Vettel.

To amma tsohon dan wasan tseren Bernie Ecclestone da ya taka rawa wurin kawo gasar Rasha, ya ce ba a yi tunani ba wurin soke gasar a can, la'akari da cewa ba yaki a ke yi a Rashar ba.

''Wannan yunkuri na hukunta Rasha a harkar wasanni ba aiki zai yi ba. Don shi Shugaba Putin ko a jikinsa. Don bai damu da wasan ba.'' In ji Ecclestone.

Tun da farko hukumomin wasannin kwallon kafa da na Olympics sun dauki matakin dakatar da Rasha da kungiyoyinta daga halartar wasannin da su ke shiryawa, saboda kutsawa cikin Ukraine.