Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Martinez, Abramovich, Suarez, Kessie, Wijnaldum, Haaland, Neves, Azpilicueta

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na fatan nasara bayan samun ƙarin-gwiwa a farautar ɗan wasan Inter Milanmai shekara 24 Lautaro Martinez, yayinda ƙungiyar ta Italiya ta nuna alamun za ta maye gurbinsa da ɗan wasan Borussia Monchengladbach Marcus Thuram mai shekara 24. (Sun)
Roman Abramovich ya karɓi tayi daga sassa da dama na turai na masu son saye Chelseadaga hannunsa kan£3bn.(PA, via Independent)
Barcelona na son gwada sa'arta kan dan wasan Wolves da ke buga tsakiya Ruben Neves. Manchester United da Arsenal su ma sun shiga sahun masu farautar ɗan wasan mai shekara 24. (Mail)
Aston Villa ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan AC Milan Franck Kessieda naAtletico Madrid Luis Suarez, mai shekara 35. (Express)
Barcelona ta yi nisa a tattaunawa kan saye Kessie, yayinda ɗan wasan Milan ke cikin jeren 'yan wasan da take farauta da kuma 'yan wasan Chelsea Andreas Christensen da Cesar Azpilicueta. (ESPN)
Chelsea ta gabatar da tayin karshe a kokarin ci gaba da rike hristensen a Stamford Bridge wanda ke son tafiya Barcelona a wannan kakar. (90min)
Villa za ta biya £21m kan ɗan wasan Paris St-Germain Georginio Wijnaldum, mai shekara 31. (Jeunes Footeux, via BirminghamLive)
Leeds United na fatan ganin sabon kocinta Jesse Marsch ya taimaka wajen daidaita saye ɗan wasan Amurka mai shekara 21 Brenden Aaronson daga Austria. (Star)
Ɗan wasan Ingila Jude Bellingham ya zaɓi tsawaita zamansa a Borussia Dortmund.(Bild, via Mirror)
AC Milan ta daidaita da Lille kan ɗan wasanta mai shekkara 22 Sven Botman.(Gazzetta dello Sport - in Italian)
Daraktan wasanni aPSG Leonardo ya yi watsi da raɗe-raɗin da ke cewa Kylian Mbappe zai koma Real Madrid ko Liverpool, ya ce ɗan wasan mai shekara 23 an ba shi sabon kwantiragi mai kwaɓi. (Liverpool Echo)
Everton, Newcastle da Leeds sun shiga jeren kungiyoyi irinsu Roma, Atalanta, Bologna da kuma Bayer Leverkusen, Borussia Dortmund daNice da ke zawarcin ɗan wasan CF Montreal mai shekara 23 Dorde Mihailovic. (Calciomercato - in Italian)
KocinBarcelona Xavi Hernandez ya tafi Jamus domin tattaunawa da Borussia Dortmundkan ɗan wasanta Erling Haaland. (Mirror)
Ɗan wasanChelsea Timo Werner mai shekara 25 na san sanin makomarsa a ƙungiyar, zai tattauna da Thomas Tuchel. (Mail)
BurinArsenalna saye ɗan wasan Moroko mai 24 Noussair Mazraoui daga Ajax ya zo karshe, bayan matashin ya bayyana cewa ba shi da niyyar komawa wata kungiyar Firimiya a Ingila. (De Telegraaf, via Sun)
Tottenham na farautar ɗan wasan dagaRB Leipzig, Josko Gvardiol. (Mail)
Komawa Arsenal ta kazance abin da Club Brugge ke nazari kan ɗan wasanta mai shekara 22 Noa Lang. (De Standaard, via TEAMtalk)
Tottenham na son saye dan wasan MiddlesbroughDjed Spence mai shekara 21. (Goal)
Arsenalta samun kwarin-gwiwa a kokarin saye Ollie Watkin mai shekara 26 daga Aston Villa.(Football Insider)



























