Dalilai 5 da suka hana shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Daga gidaje zuwa manyan masana'antu, daga ƙananan ƴan kasuwa zuwa asibitoci da makarantu, matsalar wutar lantarki na ci gaba da shafar kusan kowane fanni na rayuwa a Najeriya.

Yayin da wasu ƴan kasuwa ke kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen man fetur domin janareta, wasu masana'antu na fama da tsadar samar da kayayyaki, lamarin da ke iya shafar farashinsu a kasuwa. A gidaje kuma, rashin ingantacciyar wutar lantarki na ƙara jefa jama'a cikin wahalhalun rayuwa da haifar musu da cikas a harkokinsu na yau da kullum.

A asibitoci, da makarantu da sauran muhimman cibiyoyi, samun wutar lantarki mai ɗorewa na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata, kuma ya kan taimaka wajen ceton rayukan al'umma.

Duk wata gwamnati da aka yi a baya a Najeriya, ta yi alkawarin shawo kan wannan matsala, sai dai har kawo yanzu, tana nan daram, wasu ma na cewa tana sake taɓarɓarewa.

To shin a ina gizo ya ke saƙar ne? me ya sa har yanzu aka kasa samun wata gwamnati ko shugaba da zai share wa ƴan Najeriya wannan hawaye na su duk da maƙudan kuɗaɗen da ake zubawa a wannan fanni?.

BBC Ta tattauna da Dr Abdulrahman Umar Lawan, malami ne a sashen koyar da harkokin wutar lantarki, sannan mataimakin darakta a cibiyar samar da tsaftataccen makamashi ta Najeriya, wanda ya lasafto wasu dalilai biyar da ya kira ''Ummul-haba'isin kasa shawo kan matsalar lantarki a Najeriya''

1. Cin hanci da rashawa

A cewar masanin, matsalar cin hanci da rashawa ce a kan gaba, cikin matsalolin da ke hana shawo kan matsalar wuta a Najeriya, duba da irin ɗumbin kuɗaɗen da aka ware wa ɓangaren tun daga shekaru da dama da suka gabata zuwa yanzu.

Ya ce ''Idan aka karkatar, ko sace kuɗaɗen da aka ware domin gina cibiyoyin samar da wuta, ko gyara na'urori ko faɗaɗa hanyoyin rarraba lantarkin, to tamkar ana mayar da hannun agogo baya ne, kuma babu wani lokaci da za a kai ga warware matsalar.

''Haka kuma, idan ana bayar da kwangiloli ba bisa ƙa'ida ba, ko kuma ana fifita alaƙar siyasa da ta kashin kai maimakon ƙwarewa kamar yadda ake yawan samu a yanzu, akwai haɗarin zaɓar kamfanonin da ba su da isasshen ƙarfin gudanar da ayyukan, wato daga bisani za su gaza yin abun da ake so, ƙarshe kuma abun ya ƙare a kan al'umma.

Wani rahoton cibiyar U4 kan cin hanci da rashawa a ɓangaren wutar lantarkin Najeriya ya bayyana yadda karkatar da kuɗaɗe, da rashin gaskiya a tsarin kwangiloli da raunin hukumomin sa ido ke iya kawo cikas ga ayyukan ɓangaren.

2. Ɗumbin bashin da ke kan kamfanonin lantarki

Dr Abdulrahman Umar, ya ce matsalar basussuka na daga cikin manyan ƙalubalen da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki a Najeriya, domin kamar yadda ƴan magana kan ce ''Da ruwan ciki ake jan na rijiya''

A cewarsa ''Tsarin wutar lantarkin Najeriya ya ƙunshi kamfanonin da ke samar da ita, da waɗanda ke rarraba ta, da masu samar da kayayyaki, musamman iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da wutar''

Ya ci gaba da cewa ''Idan kamfanonin rarraba wutar lantarki ba su biya cikakken kuɗin wutar da suka karɓa ba, hakan na iya rage kuɗaɗen da ake tura wa kamfanonin samar da wuta. Idan waɗannan kamfanoni kuma ba su samu kuɗin da za su biya masu samar da gas don kula da na'urorinsu ba, hakan na iya rage ƙarfin samar da wutar''

Ya ce su kansu ƴan Najeriya ba sa maida hankali wajen biyan kuɗin wuta, domin a kowacce shekara ana bin su bashin aƙalla Naira Triliyan ɗaya.

A watan Fabrairun 2025, Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce bashin da gwamnati ke bin kamfanonin samar da wuta da na rarraba ta ya haura naira tiriliyan huɗu.

3. Rashin aiwatar da dokokin lantarki

Masanin ya ci gaba da cewa Najeriya tana da dokoki barkatai da suka shafi wutar lantarki, sai dai inda Gizo ke saƙar shine yadda ake aiwatar da dokokin da kuma rashin hukunta masu yi musu hawan ƙawara.

Idan kamfanonin wutar lantarki ba su cika yarjejeniyoyinsu ba, ko kuma ba su bi umarnin hukumomin da ke sa ido ba tare da fuskantar matakin da ya dace ba, hakan na iya raunana tsarin gudanar da harkar, domin sun latsa sun ga ruwa, wato za su iya saɓa ƙa'ida ba tare da fargabar abun da ka-je-ya-zo ba.

A cewarsa ''Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ta samar da sabon tsarin da ya ba gwamnatocin jihohi damar tsara harkokin wutar lantarki a yankunansu, bisa tanade-tanaden dokar. Wannan na buƙatar haɗin kai tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi, da kuma fayyace alhakin kowane ɓangare''

Ya ce idan har ba a samar da ingantaccen tsarin sa ido da aiwatar da dokokin da suka shafi samar da wutar lantarki ba, to kuwa za a ci gaba da fama da wannan matsala.

4. Rashin isassun kayayyakin aiki

Ƙwararren ya ce daɗin-daɗawa wani babban ƙalubale shi ne ƙarancin muhimman kayayyakin da ake amfani da su wajen aika wutar ga jama'a.

''Ko da an samar da isasshiyar wuta, dole ne kuma a samu hanyoyin rarraba ta ga mutane, kuma ana buƙatar ingantattun na'urorin rage ƙarfin wutar ta yadda za ta dace da yanayin da za a iya rarraba ta zuwa gidaje da wuraren kasuwanci.

Ya fayyace cewa idan layukan raba wuta ba su da isasshen ƙarfi, ko kuma sun lalace, ba za a iya isar da duk wutar da ake samarwa ga masu amfani yadda ya kamata ba, a irin wannan ne ake samun faɗuwar turakun wutar da ake yawan samu a Najeriya.

Rahotanni daban daban da ke bayani kan harkar wutar lantarkin Najeriya sun sha nuna cewa wannan wata babbar matsala ce da idan har ba a warware ta ba, abu ne mai yiwuwa a shawo kan matsalar lantarkin.

5. Lalata kayayyakin wutar lantarki da matsalolin tsaro

Dakta Abdulrahman Umar ya ce satar wayoyin wuta, da lalata layukan raba ta da kai hari kan kayayyakin samar da wutar ma na taimakawa wajen kawo cikas ga samarwa da isar da wutar lantarki.

''Idan aka lalata layin raba wuta ko aka sace muhimman kayayyaki, ana buƙatar lokaci da kuɗaɗe domin gyara su. A lokacin da ake gudanar da gyaran, al'ummomin da ke dogaro da wannan hanyar na iya fuskantar katsewar wuta''

Wannan na nufin cewa inganta tsaro da sa ido kan kayayyakin wutar lantarki na daga cikin matakan da ake buƙata domin samar da ingantacciyar hidima.

Ya ƙara da cewa yawan samun irin waɗannan matsaloli na iya ƙara wa kamfanonin wutar lantarki kuɗaɗen gudanar da ayyukansu, tare da karkatar da kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen faɗaɗa hanyoyin samar da wuta da inganta hidima zuwa gyaran kayayyakin da aka lalata.

Ta wacce hanya za a shawo kan matsalar?

Masanin ya bayar da wasu shawarwari da ya ce ya kamata mahukunta su bi domin shawo kan matsalar, ta yadda al'ummar Najeriya za su rayuwa cikin haske da salama.

Shawarwarin sun haɗa da

  • Ƙarfafa bincike da hukunta masu aikata cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da gaskiya wajen bayar da kwangiloli da kashe kuɗaɗen jama'a.
  • Aiwtar da dokoki da ƙa'idojin harkar wutar lantarki yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa kamfanoni da hukumomi sun cika alhakinsu.
  • Samar da tsarin biyan basussukan da ake bin kamfanonin wutar lantarki, tare da hana sabon bashi ci gaba da taruwa.
  • Zuba jari wajen gyara da faɗaɗa kayayyakin samarwa, da rarraba wuta.
  • Inganta samar da iskar gas da tsaron kayayyakin wuta.
  • Faɗaɗa tsarin awo na wutar lantarki da inganta tattara kuɗaɗe domin tabbatar da dorewar harkar.
  • Ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati, da hukumomin sa ido da kamfanonin wutar lantarki.