Mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ce sun kashe sama da ƴanbindiga 30 a wani artabu da ya ɗauki kwanaki uku bayan da maharan ɗauke da makamai suka kai wa al'ummar yankin hari.
Mazauna ƙauyen sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa maharan, waɗanda aka ruwaito sun je a kan babura, sun kewaye ƙauyen tare da buɗe wuta kan mutanen garin.
Mutanen sun ce ƴanbindigar sun kewaye ƙauyen da nufin kai masa hari, inda suka yi ƙoƙarin kare garinsu.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun isa ƙauyen ne lokacin da wasu daga cikin mazauna ƙauyen suka tafi gonakinsu domin girbe amfanin gona.
“Kafin mu ankara da abin da ke faruwa, 'yan bindigar sun riga sun kewaye ƙauyen daga kowane ɓangare, ɗauke da mutum uku a kan kowane babur ,” in ji shi.
Mutumin ya ce dama wasu daga cikin mutanen garin na cikin shirinsu, lamarin da ya sa suka fuskance su domin kare kansa daga zama ƴangudun hijira.
''Mun kashe kusan yanbindiga 30 a wannan artabu,'' kamar yadda ya shaida wa Daily Trust.
Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa a shirye take wajen tallafa wa mutanen ƙauyen wajen ba su kariya.