Amurka ta umarci ƴanƙasarta su fice daga Saudiyya
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci jami'an diflomasiyyarta da iyalansu su fice daga Saudiyya saboda barazanar hare-haren da mayaƙan Houthi ke kai wa ƙasar.
Jami'an Saudiyya sun ce an daƙile wani hari da aka kai ta sama kan wani wurin samar da man fetur.
Sai dai mutum biyu sun mutu bayan wani jirgi mara matuƙi ya faɗi, yayin da wani mutum ya mutu a wani hari da aka kai filin jirgin saman King Fahad.
Rikici tsakanin mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran da kuma Saudiyya ya ƙara tsananta tun daga watan da ya gabata.
Houthi na mayar da martani kan hare-haren Saudiyya ta hanyar kai hare-hare kan filayen jiragen sama, cibiyoyin makamashi da sansanonin soji.
Wani mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce an umarci ma'aikatan da ba sa gudanar da ayyukan gaggawa su fice daga ƙasar tare da iyalansu.
Ya ƙara da cewa rikice-rikicen da ke gudana na iya ƙara tsananta cikin gaggawa.
Rahotanni sun kuma ce mutum takwas sun jikkata sosai a harin da aka kai filin jirgin saman King Fahad.