Marouane Fellaini zai yi jinya

An wallafa

Marouane Fellaini ba zai buga wa Manchester United wasan Premier da za ta kara da Liverpool ba, sakamakon raunin da ya ji a lokacin da yake yi wa Belgium tamaula.

Tawagar kwallon kafa ta Belgium sai sauya Fellaini ta yi saura minti 16 a je hutu a karawar da ta doke Bosnia-Herzegovina a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka buga a ranar Asabar.

Tawagar Belgium za ta kara da Cyprus a wasan shiga kofin duniya a ranar Talata, yayin da United za ta ziyarci Anfield a ranar 14 ga watan Oktoba.

United za ta ziyarci Benfica a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League, sannan ta fafata da Huddersfield a gasar Premier a ranar 21 ga watan Oktoba.

Fellaini ya ci wa United kwallo hudu a kakar bana, ciki har da guda biyu da ya ci Crystal Palace a gasar Premier.