Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Peter Crouch ya kafa tarihin cin kwallo da ka
An wallafa
Dan wasan Stoke City, Peter Crouch ya shiga kundin tarihin na Guinness World Record a matsayin wanda ya fi cin kwallo da ka a gasar cin kofin Premier.
Dan wasan ya ci 51 da ka, hakan ya sa ya dara tsohon dan kwallon Blackburn da Newcastle Alan Shearer da guda biyar.
Crouch mai shekara 36, ya ci kwallo 105 a gasar Premier a wasa 436 da ya buga wa kungiyoyi shida.
Crouch ne ya ci wa Stoke City kwallon da ta doke Southampton a gasar Premier wasan mako na bakwai.