Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harry Maguire: 'Ya dace a hukunta masu nuna wa Pogba wariya'
Dan wasan Manchester United Harry Maguire ya yi kira ga kamfanonin sada zumunta "da su rika dakile munanan kalamai" bayan da aka yi wa takwaransa Paul Pobga kalaman nuna wariya domin ya barar da fanareti.
Pogba ya barar da faneriti a wasan da suka tashi 1-1 da Wolves a ranar Litinin.
Dan wasan mai shekara 26 shi ne dan kwallo na uku da ya fuskanci kalaman wariyar launin fata cikin mako guda.
Kazalika, shi ma dan wasan United Marcus Rashford ya bayyana goyon bayansa ga dan wasan Faransa, yana cewa "wannan abu ya isa haka."
"Manchester United iyali ne guda kuma Paul Pogba babba ne a cikin wannan iyalin. Idan aka taba shi, an taba kowannenmu," kamar yadda dan wasan gaban Ingila Rashford ya wallafa a Twitter.
United ta ce "tana aiki wajen gano" wadanda suke da hannun game da kalaman wariyar.
"Masu wadannan kamalai ba sa magana da yawun United kuma abin sha'awa ne ganin yadda magoya bayanmu suka yi Allah-wadai da kalaman a kafafen sada zumunta," in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar.
Kungiyar ta ce ba za ta lamunci kalaman nuna wariyar launin fata ba kuma ta ce ita ba ta nuna wa kowa wariya.
A karshe ta ce za ta dauki "tsattsauran mataki game da al'amarin kuma ta bukaci kamfanonin sada zumunta su ma su dauki mataki".