Kudi ne a gaban Uefa ba 'yan wasa ba in ji Courtois

Thibaut Courtois (right) in action for Belgium against Italy
Bayanan hoto, Courtois' Belgium were beaten 2-1 by Italy in Sunday's Nations League third-place playoff
An wallafa

Thibaut Courtois ya zargi Uefa da neman kudi mai tsoka, maimakon bukatun 'yan wasa, wanda ya ce ana daukarsu tamkar butum butumi.

Dan kwallon, Real Madrid ya buga wa tawagar Belgium wasan daf da karshe da na neman mataki na uku a lokacin hutu na kalandar Fifa.

A wasan karshe da ya buga a gasar bana shine wanda Italia ta zama ta uku, bayan da ta yi nasara a kan Belgium, inda mai tsaron ragar, mai shekara 29 ya furzar da abin da ke bakinsa.

"Wannan gasar kawai ta neman kudi ce, ya kamata ku fada wa kanmu gaskiya,'' kamar yadda ya sanar da Sky Sports.

"Mun buga ne kawai, saboda a wajen Uefa rarar samun kudi ne da suke samu ta fannin talabijin.

"A wajen mu wasa ne mai kyau tunda da Italia muka kara, haka itama Italia ke hangen hakan - amma ka kalli yadda tawagogn ke ta sauya 'yan wasa - da a ce karawar karshe ce da anga wasu 'yan kwallon ne da ban.''

Eden Hazard da kuma Romelu Lukaku ba su buga karawar ta ranar Lahadi ba, sakamakon jinya, bayan raunin da suka ji a wasa da Faransa karawar daf da karshe ranar Alhamis,

Tawagar Italiya mai rike da kofin Euro 2020 da ta lashe a bana ita ce ta yi nasara a kan Belgium da ci 2-1 da ta zama ta uku a Nations League ranar Lahadi.

Courtois ya ci gaba da cewar "Wannan na nuna maka yadda muke yin wasanni da yawa. Shekara mai zuwa za a buga gasar cin kofin duniya a Nuwamba - za kuma mu ci gaba da buga wa kungiyoyi tamaula har zuwa farkon watan Yuni - za ka iya jin rauni daga nan ba wanda zai kara damuwa da kai.

"Bayan buga wasanni da yawa a kakar tamaula, za mu kara a fafatawa hudu a Nations League sai kuma hutun mako biyu, wanda ba zai isa dan wasa ya huta ba, sannan ya fuskanci kakar da zai fara buga wa.

"Idan har ba mu ce komai ba haka za a yi ta tafiya. Su (Uefa) sun nuna bacin ransu kan wasu kungiyoyi da suka tsara buga gasar Super League, amma ba sa damuwa da bukatar 'yan wasa sai dai aljihunsu.''

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, na shirin gabatar da tsarin buga gasar cin kofin duniya duk bayan shekara bibiyu, maimakon hudun da aka saba.

"Kana jin ana cewa za a koma buga gasar Zakarun Turai da ta kofin duniya duk bayan shekara bibiyu,'' kamar yadda Courtois ya kara cewa. ''Yaushe za mu samu lokacin hutu? Babu.

"Saboda haka fitattun 'yan wasa za su ke jin a koda yaushe, kuma karshen maganar kenan. Abin da ya kamata a dauki mataki kenan, kuma mataki na sosai na hakika da zai amfani dan wasa. Mu ba butun butumi bane,''