Almeria ta bukaci yuro miliyan 60 kan Sadiq Umar

An wallafa

Almeria ta bukaci Sevilla ta biya yuro miliyan 60 idan har tana son daukar dan wasan gabanta Sadiq Umar.A cewar jaridar Estadio deportivo Sevilla na son kammala cinikin dan wasan ba tare da bata lokaci ba.Dama Barcelona da Newcastle sun nuna sha'awar daukar dan gaban Najeriyar, wanda kawo yanzu ya ci kwallaye 13 ya taimaka aka ci tara a wasanni 24.

Sadiq na cikin tawagar Super Eagles da ta wakilci Najeriya a gasar AFCON da aka yi kwanan baya a Kamaru.

Ko a kakar bara Sadiq ya ci kwallaye 20 bayan da kungiyar ta siyo shi daga Partizan Belgrade.

Hakan na nufin daga zuwansa kungiyar kawo yanzu ya ci kwallaye 33 kenan a kasa da kaka biyu.

Dan wasan gaban na da yarjejeniya da Almeria daga nan zuwa 2025, kuma fatan kungiyar shine ta samu tsallakowa gasar La Liga tare da Sadiq Umar.

To amma lura da cewa manyan kungiyoyi a La Liga kamar Barcelona da Sevilla na neman dan Najeriyar, da wahala ta iya ajiye shi a kungiyar na tsawon lokaci.