Unai Emery: Tsohon kocin Arsenal ya koma Villarreal

An wallafa

An nada tsohon kocin Arsenal Unai Emery a matsayin sabon kocin kungiyar Villarreal inda ya kulla yarjejeniyar shekaru uku.

Dan kasar Spaniya mai shekaru 48, ya maye gurbin, Javi Calleja wanda ya bar kungiyar duk da cewa ta karkare a matsayin ta biyar a kan tebur kuma za ta buga gasar.

Emery ya bar Arsenal a watan Nuwambar bara.

A can baya, ya jagoranci Sevilla da Valencia da kuma kungiyar Paris St-Germain ta Faransa.

Emery ne yam aye gurbin Arsene Wenger a watan Mayun 2018 bayan ya lashe gasar Europa sau uku a jere tare da Sevilla da kuma lashe gasar kwallon kasar Faransa tare da PSG.