Brandon Williams: Norwich City ta dauki aron mai tsaron bayan Manchester United

An wallafa

Norwich City ta kammala daukar aron mai tsaron bayan Manchester United, Brandon Williams da zai mata wasanni zuwa karshen kakar bana.

Williams, mai shekara 20, ya zama na tara da koci Daniel Farke ya dauka, tun bayan da kungiyar ta koma buga Premier League a kakar nan.

Dan kwallon ya buga wa United wasa hudu a kakar da ta wuce, kenan baya samun damar yin wasa da yawa a kungiyar.

Williams ya buga karawa 21 a Premier League, tun bayan da ya koma United, wadda ya fara yi wa wasa cikin 2019 da cin kwallo daya.

Mai tsaron bayan United yana buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21 wasanni.